Ronaldo ka iya komawa real madrid
Main Labarai LABARAIWASANNI Ana rade-radin Cristiano Ronaldo ya na son ya koma Real Madrid a day ago 3518 views by Muhammad Malumfashi Jita-jita ta na yawo cewa akwai yiwuwar Cristiano Ronaldo ya bar kungiyarsa ta Juventus, ya tattara ya koma kungiyar Real Madrid da ya bari a shekarar 2018. Tauraro Cristiano Ronaldo ya dawo Birnin Madrid a Ranar Lahadi inda ya shiga cikin ‘yan kallo na babban wasan El-Clasico da kungiyarsa ta da, ta buga da Barcelona. Rahotanni sun ce ‘Dan wasan Duniyan ya na da burin komawa kungiyar Real Madrid. Wani na-kusa da Cristiano Ronaldo mai suna Edu Aguirre ya bayyana wannan. Edu Aguirre ya ce Ronaldo ya na da burin komawa kungiyar Real Madrid da ya bari shekaru kusan biyu da su ka wuce bayan ya kafa irin tarihin da za a dade ba a karya ba. Aguirre ya bayyana cewa dawowa filin Santiago Bernabeu da Ronaldo ya yi domin ya kalli wasan El-Clasico ya nuna cewa har gobe kungiyar na cikin zuciyar ‘Dan wasan. KU KARANTA: Cristiano Ronaldo ya kalli wasan El-Clasi...