Posts

Showing posts from March, 2020

Ronaldo ka iya komawa real madrid

Image
Main Labarai LABARAIWASANNI Ana rade-radin Cristiano Ronaldo ya na son ya koma Real Madrid a day ago 3518 views by  Muhammad Malumfashi Jita-jita ta na yawo cewa akwai yiwuwar Cristiano Ronaldo ya bar kungiyarsa ta Juventus, ya tattara ya koma kungiyar Real Madrid da ya bari a shekarar 2018. Tauraro Cristiano Ronaldo ya dawo Birnin Madrid a Ranar Lahadi inda ya shiga cikin ‘yan kallo na babban wasan El-Clasico da kungiyarsa ta da, ta buga da Barcelona. Rahotanni sun ce ‘Dan wasan Duniyan ya na da burin komawa kungiyar Real Madrid. Wani na-kusa da Cristiano Ronaldo mai suna Edu Aguirre ya bayyana wannan. Edu Aguirre ya ce Ronaldo ya na da burin komawa kungiyar Real Madrid da ya bari shekaru kusan biyu da su ka wuce bayan ya kafa irin tarihin da za a dade ba a karya ba. Aguirre ya bayyana cewa dawowa filin Santiago Bernabeu da Ronaldo ya yi domin ya kalli wasan El-Clasico ya nuna cewa har gobe kungiyar na cikin zuciyar ‘Dan wasan. KU KARANTA: Cristiano Ronaldo ya kalli wasan El-Clasi...

Chelsea ta kori Liverpool a fa

Image
Kungiyar Chelsea ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a FA Cup, bayan da ta doke Liverpool da ci 2-0 ranar Talata a Stamford Bridge. Chelsea ta fara cin kwallo ta hannun Willian Borges Da Siva minti na 13 da fara tamaula, sannan Ross Barkley ya ci na biyu a zagaye na biyu Wannan ne karo na biyu ajere da aka doke Liverpool, bayan 3-0 da Watford ta yi nasara a kanta a gasar Premier a karshen mako. Liverpool ta yi sauyin 'yan wasa bakwai daga wadanda suka buga karawa da Watford ranar Asabar - bayan da ta yi wasan Premier 18 a jere ba a doke ta ba. Kungiyoyin biyu sun kara a bana sau biyu, inda suka yi 2-2 a European Super Cup ranar 14 ga watan Agustan 2019. Sun kara haduwa a wasan Premier a Stamford Bridge ranar 22 ga watan Satumba, inda Liverpool ta yi nasara da ci 2-1. Bayern Munich ta saka Chelsea cikin matsi Dalilai 5 da suka sa aka yi nasara a kan Liverpool Watfod ta hana Liverpool cin wasan Premier na 19 a jere Liverpool tana nan a matakinta na daya a kan teburin...