Chelsea ta kori Liverpool a fa

Kungiyar Chelsea ta kai wasan daf da na kusa da na
karshe a FA Cup, bayan da ta doke Liverpool da ci 2-0 ranar Talata a Stamford Bridge.
Chelsea ta fara cin kwallo ta hannun Willian Borges Da Siva minti na 13 da fara tamaula, sannan Ross Barkley ya ci na biyu a zagaye na biyu
Wannan ne karo na biyu ajere da aka doke Liverpool, bayan 3-0 da Watford ta yi nasara a kanta a gasar Premier a karshen mako.
Liverpool ta yi sauyin 'yan wasa bakwai daga wadanda suka buga karawa da Watford ranar Asabar - bayan da ta yi wasan Premier 18 a jere ba a doke ta ba.
Kungiyoyin biyu sun kara a bana sau biyu, inda suka yi 2-2 a European Super Cup ranar 14 ga watan Agustan 2019.
Sun kara haduwa a wasan Premier a Stamford Bridge ranar 22 ga watan Satumba, inda Liverpool ta yi nasara da ci 2-1.
Bayern Munich ta saka Chelsea cikin matsi
Dalilai 5 da suka sa aka yi nasara a kan Liverpool
Watfod ta hana Liverpool cin wasan Premier na 19 a jere
Liverpool tana nan a matakinta na daya a kan teburin Premier da maki 79 da tazarar maki 22 tsakaninta da Manchester City mai biye da ita.
Ita kuwa Chelsea tana ta hudu a kan teburin Premier da maki 45 da tazarar maki 34 tsakaninta da Liverpool.
Chelsea za ta karbi bakuncin Everton a wasan gaba a gasar Premier, sannan ta ziyarci Aston Villa, sai kuma ta ziyarci Bayern Munich a gasar Champions League wasa na biyu ranar 18 ga watan Maris.
Liverpool kuwa za ta karbi bakuncin Bournemouth a wasanta na Premier na gaba, sannan ta fafata da Atletico Madrid a wasa na biyu a Champions League.

Atletico Madrid ta doke Liverpool da ci 1-0 ranar 18 ga watan Fabrairu a Spaniya

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Ronaldo ka iya komawa real madrid